Hadarurrukan ababen hawa sun kashe mutum 1,223 a Jamhuriyar Nijar – Rahoto

0
116

Hukumar kiyaye hadarurrukan ababen hawa ta Jamhuriyar Nijar, ANISER, ta ce mutum dubu daya da dari biyu da ashirin da uku ne suka rasu sanadin hadarurruka a 2022.

Ta bayyana haka ne ranar Litinin a sabon rahoto na shekara-shekara da ta fitar kan yawan hadarurrukan ababen hawa a kasar.

Rahoton, wanda shugaban hukumar Malam Abdou Mahamane, ya fitar ya bayyana cewa a 2022 an samu aukuwar hadarurruka 8,561 a 2022.

Rahoton ya nuna cewa an samu karuwar hadarurruka da 13%.3 cikin 100% idan aka kwatanta da shekara ta 2021 yana mai cewa a 2021 an samu hadarurruka 7543 inda mutum 1153 suka mutu.

Ya ce dubban mutane ne suka jikkata sakamakon hakan.

ANISER ta kara da cewa rashin aiki da ka’idojin tuki da gudun-wuce-sa’a na cikin abubuwan da suka haddasa yawan hadarurrukan ababen hawa a Jamhuriyyar ta Nijar.

Rahoton ya yi kira ga al’ummar kasar su mayar da hankali wurin bin doka yayin da suke tuki.

Jamhuriyar Nijar na cikin kasashen da ke fama da karancin hanyoyi masu kyau, ko da yake gwamnati ta ce tana aiki tukuru domin magance matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here