Kotu ta samu tsohon shugaban Amurka da laifin cin zarafin lalata

0
41

Masu taya alƙali hukunci sun samu tsohon shugaban Amurka Donald Trump da laifin auka wa wata mai rubuta sharhi a mujalla da lalata a wani kantin sayar da kaya na birnin New York a shekarun 1990.

Masu taya alƙali hukunci sun kuma samu Donald Trump da ɓata wa E Jean Carroll suna a watan Oktoban 2022 a dandalinsa na sada zumunta mai suna Truth, inda ya bayyana zarge-zargen nata a matsayin “damfara”.

Matar mai suna E Jean Carroll, ‘yar shekara 79, ta ce Trump ya auka mata ne a kantin Bergdorf Goodman da ke unguwar masu hannu da shuni ta Manhattan a ƙarshen 1995 ko kuma a farkon 1996.

A cewarta, sun yi karo da juna a lokacin da suka je kantin sayayya.

Daga nan, sai ta yi zargin cewa Trump ya nemi jin ra’ayinta sa’ar da ya je sayen rigar mama da ɗan kamfai don wata matar daban, inda cikin tsokana ya nemi ko za ta gwada don ganin dacewar kyawun tufafin.

Sai dai suna shiga ɗakin canza tufafi, Carroll ta yi iƙirarin cewa hamshaƙin mai arziƙin gine-ginen ya auka mata, inda ya tokare ta a bango, kuma ya ci zarafin ta.

Carroll, wadda ta riƙa wallafa sharhi mai taken “Ask E. Jean” a mujallar Elle daga 1993 zsuwa 2019, ta yi iƙirarin cewa ta yi ƙoƙari, ta tunkuɗe Trump bayan an sha “matuƙar gaganiya”.

Ba ta kai rahoton zargin wannan al’amari ga ‘yan sanda ba, kamar yadda takardar ƙorafinta ta nuna, saboda ta yi matuƙar “gigicewa kuma ta yi fatan kada ta ɗauki kanta a matsayin wadda aka yi wa fyaɗe”.

Masu taya alƙali yanke hukuncin dai sun ce ba su samu Donald Trump da laifin yi wa E Jean Carroll fyaɗe ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here