An ɗaure wani saurayi kan laifin kashe tsohuwar budurwarsa

0
101

An yanke ma wani saurayi hukuncin daurin rai-da-rai bayan an same shi da laifin kisan kai, inda ya daba wa wata mata wuka har sau 40 a yammacin birnin Landan

Dennis Akpomedaye, mai shekara 30 da haihuwa, ya kashe Anna Jedrkowiak ‘yar asalin Poland mai shekara 21 da haihuwa a wani lungu a yankin Ealing, a watan Mayun bara.

Kotun Kingston Crown ta samu bayanin cewa Anna ba ta dade da rabuwa da Dennis a matsayin budurwarsa ba, inda ta tattara ta koma birnin Landan.

Akpomedaye, wanda ke zama a garin Newport da ke birnin South Wales ya gano Jedrkowiak, ya jira ta taso daga aiki kafin ya biyo ta a lokacin da take tare da wani saurayi mai suna Jack Maskell wanda ya shaida kisan.

Kotu ta ce Akpomedaye ya nemi ya sare mata kai baki daya inda ya ci gaba da daba mata wuka.

Mista Maskell dan shekara 21 wanda ke aiki a wuri daya da wadda aka kashe kuma suke tafiya tare a lokacin da kisan ya afku, ya shaida wa kotu cewa abin ya sa ya shiga mummunan halin jimamin da ba zai taba mantawa ba.

“Abin babu kyawun gani. Ba zan taba manta abin da ya yi ma ta ba”

Mista Maskell ya ce ganin kisan da ya yi ya haddasa masa fuskantar mummunan matasalolin tunani da jimami.

Mahaifiyar Ms Jedrkowia, mai suna Danuta da ke zama a kasar Poland ta shaida wa kotu a wata sanarwa da ta aiko cewa “Wannan mai kisan kan, yana raye, kuma zai ci gaba da rayuwa na tsawon wasu shekaru, duk da cewa ya karar da rayuwar diyata”.

Ta ce Mummunan yanayin kisan da aka yi wa diyarta ya sanya ta a wani halin tsananin bakin ciki.

Da ta ke bayani a harabar kotun yayar Ms Jedrkowiak, Katareyna Glowacka ta ce Akpomedaye cikakken rago ne saboda ya kasa halartar zaman yanke masa hukunci.

“Ya aikata laifi amma ba zai iya fuskantar mu ba, ba zai iya kallon idanuwan mu ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here