Benzema na nazarin tafiya Saudiyya kan tayin £346m, Liverpool na zawarcin Kone

0
70

Ɗan wasan Real Madrid Karim Benezema mai shekara 35, na nazarin karɓan tayin albashi yuro miliyan 400 (£346m) da ya samu daga Saudiyya. (ESPN)

Arsenal ba ta da niyyar cefanar da Emile Smith Rowe, mai shekara 22 a wannan kaka, inda take fatan ɗan wasan da ke jinya ya farfaɗo nan bada jimawa ba. (Athletic – subscription required)

Kocin Tottenham Hotspur Luis Enrique na tattaunawa da kungiyar da ta lashe Seria A Napoli, sai dai kocin da ya taɓa horar da Barcelona ya fi son ya koma firimiyar Ingila. (Guardian)

Tottenham da Newcastle na zawarcin ɗan wasan Leicester mai buga tsakiya James Maddison da kuma Harvey Barnes, mai shekara 25, kowanne su an kiyasata kuɗinsu a kan £40million. (Sun)

Manchester City da Arsenal na bibbiyar ɗan wasan Leeds United da Italiya Wilfried Gnonto, mai shekara 19. (Calciomercato – in Italian)

Manchester United ba za ta cimma yarjejeniyar dindindin da ɗan wasan gaba a Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 30, da bai buga tsakiya a Austria Marcel Sabitzer.(Mail)

Ɗan wasan Real Valladolid daga Sifaniya Ivan Fresneda, mai shekara 18, ya samu tayi mai gwaɓi daga Arsenal. (BILD – in German)

Mai bugawa Faransa Benjamin Pavard, mai shekara 27, na shirin barin Bayern Munich zuwa Inter Milan. (Fabrizio Romano)

Aston Villa na kwadayin ɗan wasan Real Madrid Marco Asensio, wanda ake sa ran ya bar kungiyar bayan karewar kwantiraginsa. Ɗan wasan mai shekara 27 daga Sifaniya ya kuma ja hankalin Paris St-Germain da Arsenal da AC Milan. (Sun)

Liverpool na harin ɗan wasan Borussia Monchengladbach Manu Kone, inda aka kiyasata tsadar ɗan wasan mai shekara 22 kan yuro miliyan 40. (BILD – in German)

Juventus na kan gaba a gabatar da tayi kan ɗan wasan Chelsea Christian Pulisic mai shekata 24, kan $25m (£20.1m). (Mail)

Mai tsaron raga a FC Porto Diogo Costa, mai shekara 23, na son tafiya Manchester United, yayinda shi ma David de Gea, mai 32, ke son sanya hannu a sabon kwantiragi. (Mirror)

Wolves ta bi sahun Chelsea da Crystal Palace a zawarcin ɗan wasan Gambia Adama Bojang, mai shekara 19, da ke taka leda yanzu haka a kungiyar Gambia ta Steve Biko FC. (Standard)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here