CBN ya musanta jita-jitar karya darajar kudin kasar zuwa Naira 631 kan dala guda

0
120
Dollar-and-Naira
Dollar-and-Naira

Babban bankin Najeriya ya musanta rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, wanda ya bayyana cewar ya rage darajar kudin kasar zuwa Naira 631 akan kowace dala guda, daga yau 1 ga watan Yunin shekarar 2023.

Sanarwar da darakatan yada labaran bankin Najeriyar Isa AbdulMumin ya fitar, ta ce ko kadan babu gaskiya cikin rahoton, wanda ga dukkanin alamu an so yin amfani da  shi ne wajen haifar da rudani, sakamakon rashin sanin da yake damun kafar  watsa labaran da ta wallafa rahoton.

Babban bankin Najeriyar ya kara da cewar darajar dala akan kowace Naira na nan akan 465 sabanin 631 da aka yada cewar shi ne sabon tsarin a canjin kudin da ya fara aiki a yanzu.

Daga karshe sanarwar ta shawarci dukkanin kafafen watsa labarai da su rika tuntubar  babban bankin Najeriyar, domin tabbatar da hujjoji ko bayanan da suke neman amfani da su, musamman akan batun da ya shafi hada hada ko canjin kudade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here