’Yan bindiga sun sace ’yan mata fiye da 30 a Zamfara

0
89

’Yan bindiga sun sace ’yan mata fiye da 30 tare da kashe mutane da dama yayin wani hari da suka kai Karamar Hukumar Maradun da ke jihar Zamfara.

Maharan sun kai hari kauyukan Sakkida da Janbako a ranar Asabar da rana inda suka kashe mutum sama da 20 a Sakkida tare da jikkata karin wasu.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, an dauki ’yan mata fiye da 30 a kauyen Gora a yayin da suka tafi yin itace a dajin Daggera.

A cewarsa, ’yan bindigar sun bayar da sanarwa tun kafin sace yaran cewa idan har muna so mu yi noma a Daggera a bana, to sai mun zauna mun yi sulhu da su, kuma mun yi ta sulhu da su amma bamu san dalilin sace mana yaran ba.”

“Har kawo yanzu dai bamu ji daga garesu a kan yaran ba, amma jami’an tsaro sun bi bayansu sai dai ba wani labari,” inji shi.

Shi ma wani mazaunin Janbako, ya shaida wa BBC cewa, suna zaman lafiya sai ga sanarwa ta zo daga kauyen da ke kusa da su wato Sakkida cewa barayi sun shiga suna so a kai musu dauki.

Ya ce, “Ba tare da bata lokaci ba, mutanen kauyenmu da ‘yan sa-kai suka dauki makamai aka tunkari garin, suna isa garin ashe barayin dajin sun yi musu kwanton bauna, nan suka bude musu wuta aka kuma kashe mutane, don mu a garinmu an yi jana’izar mutane sun kai 22.”

Mutumin ya ce, an kira jami’an tsaro amma suka ce ba za su samu damar zuwa ba a daidai lokacin saboda motarsu ta yaki da suke amfani da ita bata nan.

Ya ce, daga bisani bayan jami’an tsaron sun zo sun bi barayin amma sai suka dawo da Babura biyu kawai na barayin.

“ Akwai mutane da dama da suka jikkata, kuma mu a Janbako, babu wani jami’in tsaro da ke kwana da mu ko yake zaune a garin.”

Rundunar ’yan sandan Najeriya a jihar ta Zamfara ta tabbatar wa BBC kai harin amma ta ce ba ta da karin bayani tukunna.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare haren ‘yan bindiga da satar mutane don neman kudin fansa.

Kazalika hare haren ‘yan bindiga kan tilastawa mazauna yankunan jihar zama ba tare da noma gonakinsu ba, abin da mazauna yankunan ke kokawa akai ke nan kullum.

A ko da yaushe mutanen dai su na neman daukin gwamnati a kan wannan matsalar.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here