‘Yan bindiga sun kashe mutane 24 a jihar Zamfara

0
58

‘Yan bindiga a Najeriya sun kashe mutane 24 a wasu kauyuka biyu na yankin Maradun a jihar Zamfara a wasu hare-hare mabanbanta da suka kai ranar Asabar.

Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Janbako da Sikida, an kashe mutane uku a Sikida yayin da aka kashe 21 yawancinsu ‘yan sakai a Janbako, wasu bayanai suka ce an sace mata sama da 30.

Rahotanni suka ce ‘yan ta’addan sun fito ne daga dajin da ke hade yankunan Maradun, Bakura, Kaura Namoda da Shinkafi duk a jihar ta Zamfara.

Wata Majiyar ta ce wasu ‘yan sa kai na al’ummar Janbako ne suka hada kai suka nufi Sikida domin taimakawa wajen yakar ‘yan ta’addan, amma da aka kashe da dama daga cikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here