EFCC ta kama ‘yan damfara 28 a Kuros Ribas

0
120

Jami’an hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC), sun kama wasu tagwaye, da wasu mutane 26 bisa zargin damfara a Intanet a Kalaba jihar Kuros Riba.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 6 ga watan Yuni, biyo bayan sahihan bayanan sirri da ke alakanta su da zargin damfara a Intanet.

Sauran mutane 26 da ake zargin sun hada da: Takwan Emmanuel, Kelvin Onedu, Evans Edwin, David Osuji, Osang Tony, Confidence Oblech, Uche Chinedu, Gabriel Kanong, Ojong Victor, Ephraim Ikechukwu da Shedrack Mfon.

Sauran sun hada da Godswill Omini, Walter Opha, Godswill Iti, Moses Sha, Prince Uba, Anyi Bassey, David Disi, Peter Silas, Christian Uche, Chidindu Oforji, Kelvin Anyanwu, Anthony Ojone, Samuel Disi, Gideon Joseph da Ezekiel Francis.

Sanarwar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun kware wajen damfara, wasu kuma sun aikata zamba cikin aminci.

Abubuwan da aka kwato daga gare su sun hada da wayoyin hannu, kwamfutoci, motoci biyar da sauransu.

EFCC ta ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here