Real Madrid ta gabatar da Jude Bellingham a gaban magoya baya ranar Alhamis a birnin Madrid.
Ɗan ƙwallon tawagar Ingila ya koma Real da taka leda ne daga Borussia Dortmund a kan fam miliyan 88.5 bisa yarjejeniyar buga wasa tsawon kaka shida.
Ɗan wasan Ingila mai shekara 19, ya koma Dortmund daga Birmingham City a watan Yulin 2020, kuma ya kasance ɗan wasan Ingila mafi haskakawa a gasar cin kofin duniya da aka yi bara.
Real Madrid ta bai wa Bellingham riga mai lamba biyar wadda Zinedine Zidane ya yi amfani da ita a ƙungiyar.
Bayan Zidane ya bar taka leda a ƙungiyar, mai tsaron baya, Jesus Vallejo ne ya gaji rigar, amma Belligham ya roƙe shi da cewar yana son amfani da lambar.
Shi dai Bellingham ya saka riga mai lamba 22 a Borussia Dortmund.
Ɗan wasan Ingila, wanda ya koma Sifaniya da taka leda, bayan kaka uku a gasar Jamus zai sa riga, ba mai lamba 22 ba a karon farko.
Ɗan shekara 19 ya fara sa lamba 22 tun yana matashi a Birmingham City, wadda ta jingine amfani da lambar bayan ta sayar da shi ga Dortmund a 2020.
Mai tsaron baya ɗan ƙasar Jamus, Antonio Rudiger, shi ne ke amfani da lamba 22 a Real Madrid yanzu haka.
Lokacin da Bellingham ya bar Birmingham zuwa Dortmund a kan fam miliyan 25 daga gasar Championship, shi ne mai shekara 17 da aka saya da tsada a lokacin.
Bellingham ya buga karawa 42 bana a Dortmund – ya ci ƙwallo 14 ya bayar da bakwai aka zura a raga.