Me ya sa shugabannin EFCC ‘ba sa wanyewa da hukumar lafiya’?

0
89

Abdulrasheed Bawa, wanda aka dakatar daga mukaminsa na shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, shi ne na shida a cikin jerin shugabannin da suka jagoranci hukumar tun da aka kafa ta.

Kuma kusan dukkan wadanda suka shugabanci hukumar an cire su ne ba tare da son ransu ba ko kuma ba zato ba tsammani, a wani yanayi na nuna ba a yi da su.

Ranar Laraba ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Bawa, wanda aka nada a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, kuma yanzu haka yana hannun hukumar tsaro ta DSS inda ake bincike a kansa.

Wannan lamari ya bai wa wasu ‘yan Nijeriya mamaki inda suke ta muhawara da kuma tambayoyi musamman a shafukan sada zumunta cewa “Shin me ke faruwa da kujerar shugabancin wannan hukuma ne da “yawanci ba a wanyewa da ita lafiya”?

Shugabannin EFCC

Nuhu Ribadu ne ya fara aiki a matsayin shugaban hukumar ta EFCC daga shekarar 2003 zuwa 2007.

A lokacinsa hukumar ta yi suna wajen kamawa tare da gurfanar da manyan mutane da ake zargi da wawushe kudin kasa a gaban kotu, sabanin yadda ake yi kafin wannan lokacin.

Daya daga cikin manyan mutanen da hukumar ta gurfanar a gaban kotu shi ne Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya na lokacin, Tafa Balogun, kuma kotu ta same shi da laifi.

Haka kuma EFCC, karkashin jagorancin Nuhu Ribadu, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori a gaban kotu a wani babban zargi na cin hanci da ya kai shi ga karewa a wata kurkukun Birtaniya.

Sai dai kuma a shekarar 2007 ne aka cire Nuhu Ribadu daga shugabancin hukumar kuma aka maye gurbinsa da Ibrahim Lamorde a matsayin shugaban EFCC na riko, wanda a lokacin shi ne shugaban gudanarwa na hukumar.

Ibrahim Lamorde ya rike mukamin daga watan Janairun shekarar 2007 zuwa watan Mayun shekarar 2008 lokacin da aka maye gurbinsa da Farida Waziri. Duk su biyun an nada su ne a lokacin mulkin Umaru Musa ‘Yar adua.

Bayan ta karbi Lamorde, Farida Waziri ta yi aiki a matsayin shugabar hukumar daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2011.

Cikin manyan nasarorin da ta samu shi ne kama shugabar tsohon Bankin Oceanic ta wancan lokacin, Cecilia Ibru, inda kotu ta yanke mata hukuncin daurin wata shida ta kuma umarce ta da biyan dala biliyan 1.2.

Sai dai kuma a lokacin da Shugaba Jonathan ya sauke ta daga mukamin a shekarar 2011 bayan da aka yi zargin cewa tana nuna wariya wajen yaki da cin hanci da rashawa, sannan an yi ta samun takun-saka tsakaninta da Ministan Shari’a na lokacin, Mohammed Bello Adoke.

Ibrahim Lamorde aka sake mayarwa bayan an cire ta.

Lamorde ya fara aiki a matsahin shugaban hukumar na riko amma daga bisani aka tabbatar masa da mukamin, kuma ya rike mukamin ne zuwa watan Nuwamban shekarar 2015.

Shugaba Buhari ne ya maye gurbin Lamorde da Ibrahim Magu a matsayin shugan riko na hukumar a shekarar 2015.

Wani mai sharhi ya ce kokarin wuce makadi da rawa na shugabannin hukumar wajen tuhumar wasu cikin gwamnati da ake ganin ba su da gaskiya na cikin dalilan da ke sa suke fadawa a wannan halin. Hoto: EFCC 

A watan Yulin shekarar 2020 aka cire Ibrahim Magu daga matsayinsa na shugaban hukumar EFCC na riko sannan aka kama shi bisa zarge-zarge 22 da ke da alaka da cin hanci da almubazzaranci.

An nada Mohammed Umar Abba a matsayin shugabn riko na EFCC don maye gurbinsa.

A shekarar 2021 aka maye gurbin Mohammed Umar Abba da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC.

Kuma ranar 14 ga watan Yuni aka dakatar da shi daga kan mukaminsa sannan aka soma bincike a kansa. Hasalima ya shiga hannun DSS wadda ta ce tana ci gaba da bincike a kansa.

Me ya sa ba sa wanyewa lafiya ne?

Kabiru Saidu Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan jama’a a kan shugabanci na gari da kuma tabbatar da adalci (CAJA), ya ce hakan ba ya rasa nasaba da irin yadda ake ganin gwamnati tana amfani da hukumar tamkar karen farauta kan ‘yan adawa.

“Wani lokacin tun kafin gwamnatin da ta nada mutum ya tafi sai ka ga ita kanta an fara samun takun saka kamar yadda muka gani ga shi malam Ibrahim Magu wanda shi ne ya ba wa Abdulrasheed Bawa (daga baya),” in ji Kabiru Dakata.

Ya kara da cewa zargin cin hancin da ake yi wa shugabannin hukumar na cikin dalilan da ke sa ake cire su daga shugabancin EFCC din ba tare da sonsu ba.

“Ko a baya-bayan nan mun ji cece-kuce da ya barke tsakanin tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da shi Abdulrasheed Bawa, inda Matawalle ya yi zargin cewa Bawa ya nemi ya ba shi cin-hanci,” a cewar Kabiru Dakata.

Har ila yau ya ce kokarin wuce makadi da rawa na shugabannin hukumar wajen tuhumar wasu cikin gwamnati da ake ganin ba su da gaskiya na cikin dalilan da ke sa suke fadawa a wannan halin.

Kabiru ya kara da cewa irin yadda ake amfani da shugabannin hukumar wajen farautar abokan hamayya na cikin gwamnati da na waje yakan zamanto musu matsala idan wadanda aka yi farautar sun sami iko.

Mafita

Shugaban na CAJA yana ganin ya kamata a daina kadaita shugabancin hukumar ga ‘yan sanda ko kuma ma’aikatan hukumar kawai.

“Ya kamata a nemi sahihan mutane masu gaskiya wadanda ba su da tsoro a duk inda suke a ba su ragamar hukumar.

“Mun gani wasu jami’an gwamnati da yawa suna aiki amma ba su bari an juya su domin cin amanar kasa ko yi wa wani dan Adam hidima don a ci zarafin wani ba,” in ji shi.

Ya ce, kamata ya yi, a kara wa ofishin karfi ta yadda zai yi wahala wani da yake ciki ko wajen gwamnati zai iya yin amfani da kujerar domin cimma burinsa.

Daga baya ya ce ya kamata a kara inganta tsarin walwalar aikin ma’aikatan hukumar ta hanyar biyansu albashi da alawus-alawus da ya kamata don kauce wa zargin da ake yi wa ma’aikatan cewa suna amfani da kwarjinin hukumar wajen karbar na goro a hannun mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here