Ministan harkokin wajen Saudiyya ya tattauna da Raisi na Iran

0
109

Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal Bin Farhan, ya isa Tehran tare da tattaunawa da shugaban Iran da kuma Ministan harkokin waje Ebrahim Raisi da Hossein Amir Abdolliah.

Wannan ce zaiyarar farko da wani babban jami’in Saudiyya ya kai Iran cikin shekara bakwai da ƙasashen biyu suka yanke alaƙa da Juna.

A yau, an yi taron ‘yan jarida na haɗin gwiwa tsakanin Ministan harkokin wajen Saudiyya da kuma Amir Abdolliah.

A tattaunawar, Faisal Bin Farhan ya ce ziyarar tasa na da nufin kammala duka yarjeniyoyin ƙasashen biyu a wani ɓangare na sabunta alaƙarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here