Jaruma Mercy Aigbe ta sauke farali a Saudiyya bayan ta musulunta

0
185
Mercy-Aigbe-hajj
Mercy-Aigbe-hajj

Jarumar masana’antar shirya fina-finai ta kudancin Nijeriya, Nollywood, Mercy Aigbe ta wallafa hotunanta da kanta da ke nuna ta na gudanar da Ibadar aikin Hajji a kasa mai tsarki ta Saudiyya

Jarumar wacce cikin godiyar Allah take nuna alfarinta da kasancewa cikin musulunci tare da addu’ar Allah ya karbi ibadun bayinsa.

Idan za a tuna dai Mercy Aigne ta Musulunta ne bayan da ta auri wani mai yin film, Kazeem Adeoti a shekarar 2022.

A cikin hotunan da ta wallafa a shafinta na Instagram, ta na tare da mijinta, Adeoti.

Ta rubuta da cewa, “Muna addu’ar Allah ya amshi ibadunmu a wannan rana ta musamman ta Ibada, amin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here