Matasa da dama masu hali a Najeriya kan guje wa yin layya saboda dalili na ‘rashin aure’ duk da yake suna da halin yin ibadar.
Layya, kamar yadda malamai ke faÉ—a, sunna ce mai karfi da addinin Musulunci, wanda ya É“ukaci baligai maza da mata masu dama su yi a kowace Babbar Sallah.
Sai dai matasa da dama na ganin tun da ba su da aure tamkar ba ta wajaba ba ne a kansu.
Baya ga rashin aure, matasan na bayyana dalilai daban-daban da suke ganin shi ke hana su yin layyar.
wani matashi da ke aikin gwamnati ya ce baya ga rashin aure, akwai wasu ƙarin matsalolin da suka haɗar da ɗawainiyar karatu da yake yi wa kansa.
Ya Æ™ara da cewa: ”Dama kam alhamdulillahi ina da ita, domin ina É—aukar albashi duk wata. Amma matsalar yanzu akwai dinkin sallata da na budurwata da dai sauran matsalolina na rayuwa”.
‘Rashin nutsuwa’
Ita ma wata matashiya mai suna Amina, wadda ke sana’ar sayar da kayan abinci ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta, ta ce ba ta layya ne saboda ba ta da kwanciyar hankali kasancewar ba ta da aure.
”Idan kana da aure, to kana da nutsuwa domin kuwa wasu nauyin da ke kanka, sun sauka daga wajenka sun koma kan miji. Za a kula da ke a ba ki duk abin da kike so. To ka ga ke nan kasuwancin naka ma zai samu bunÆ™asa”, in ji matashiyar mai shekara 24.
Shi kuwa wani matashin mai suna Abdulkarim Musa ya ce ba ya layya ne saboda rashin aure, sannan kuma akwai abubuwa masu yawa a gabansa.
A nata É“angaren, Farida Muhammad matashiya ce mai sana’ar sayar da kayan awarwaro, ta ce ba ta yin layyar ne kasancewar tana ririta sana’ar da take yi.
”HaÆ™iÆ™a ina da damar yin layya, amma kasancewar ba ni da aure, ya sa ba na yin layyar”.
”Haka kuma idan na É—auki wasu kuÉ—i daga cikin jarina na ce zan yi layya, yadda raguna ke tsada a yanzu, to wataÆ™ila kuma bayan sallar na rasa jarina”, in ji matashiyar.
Me addini ya ce game da layyar matasa marasa aure?
Sheikh Sulaiman Datti, babban limamin masallacin Juma’a na Sunna da ke Birnin Kudu, ya ce Musulunci cewa ya yi idan mutum yana da hali to ya yi layya ba a ware mai aure ko maras aure ba.
“Akwai hadisin manzon Allah (SAW) da ke cewa duk wanda ke da damar yin layya, amma ya Æ™i yi, to kada ya kusanci masallatanmu,” a cewarsa.
Malamin ya ce idan aka dogara da wannan hadisi layya ta zama wajibi ga duk mutumin da yake da damar yi, mace ko namiji, saurayi ko budurwa.
Malamai da dama na kokawa kan rashin yin layyar tsakanin matasa, ganin yadda matasan ke riƙe manyan wayoyi masu tsada da ababen hawa kama da daga motocin hawa zuwa baburan hawa.
Malamai da dama na kokawa kan rashin yin layya tsakanin matasa duk da yadda suke sayen manyan wayoyi masu tsada
Sheikh Dakta Abdullahi Gadon Ƙaya na daga cikin malaman da ke da wannan ra’ayi.
Cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga shehin malamin na kira ga matasa su dinga yin layya, matuƙar Allah Ya hore musu yadda za su yi.
Ya ce: ”Sai ka ga mutum yana É—inka shadda mai tsada, yana hawa babur na dubban É—aruruwa, amma sai ka ga mutum ba ya layya saboda wai ba shi da aure”.
Malamin ya kuma gargaÉ—i matasan da cewa “ku ji tsoron Allah, domin kuwa Allah Zai kama ku”.
”Duk wanda ke da halin yin layya, ya je ya yi layyarsa. Da mai aure da maras aure, kowa ya samu dama ya yi. Sallar nafila ba ka yi, sai kana da aure”? kamar yadda ya Æ™alubalanci matasan.