Jirgin farko na alhazan Najeriya ya taso daga Jeddah zuwa Sokoto da ƙarfe 1:55pm agogon Saudiyya.
Hukumar aikin Hajji ta ƙasa NAHCON ta sanar da tashin jirgin ranar Talata.
NAHCON ta ce jirgin na kamfanin Fly Nas na ɗauke da alhazai 426 da jami’i ɗaya.
Ana sa ran kammala kwaso alhazan Najeriya 95,000 nan da 3 ga Agusta.