‘Yan Najeriya na kumfar baki a kan ‘ɓacewar sabbin takardun Naira’

0
263

‘Yan Najeriya suna bayyana damuwa kan yadda sabbin takardun kuɗin ƙasar wato naira suka ɓace daga hannun jama’a wata biyar bayan ƙaddamar da su.

Tun bayan komawa amfani da tsoffin takardun kuɗi na naira 200 da 500 da kuma 1000 ne, sabbin takardun nairorin suka fara wuyar gani a birane.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito wasu mazauna babban birnin Abuja suna kokawa a kan ƙarancin sabbin takardun kuɗin.

A ranar 3 ga watan Maris ne Kotun Ƙolin Najeriya ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sababbin takardun kudin naira 200, da 500 da kuma 1,000 har zuwa ƙarshen watan Disamban bana.

Wani mazaunin Garki a Abuja, Gabriel Daniel ya ce a yanzu tsoffin kuɗi kawai ake samu a kasuwanni da na’urorin cirar kuɗi.

Wani mazaunin Nyanya, Moses Nnegedu ya ce karon ƙarshe da ya ga sabuwar takardar kuɗi ya kai mako biyu, ya ƙara da cewa a gaskiya ba a samun su.

“Ga alama ana ɓoye sabbin takardun kuɗin ne”, in ji shi.

Ya ce matuƙar Babban Bankin Najeriya da gaske yake yi wajen cimma manufar tabbatar da ganin sabbin kuɗin sun wadata a hannun mutane kafin wa’adin da sanya, kamata ya yi ya riƙa bibiyar bankunan kasuwanci.

Wani Abba Moses ya ce masu maƙudan kuɗin da suka samu sabbin takardun nairorin ne tun farko suke ɓoye kuɗin saboda tunanin wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗi a watan Disamba.

A cewarsa ko da bankuna sun fitar da sabbin kuɗin, amma wasu mutane suna samu, suna ɓoyewa, to ba lallai ne a samu wadatar su a hannun jama’a ba.

Abba Moses ya ce a makon jiya, sau ɗaya ya ga sabuwar takardar naira 500.

Shi kuwa Manasseh Gimba cewa ya yi karon ƙarshe da ya ga sabuwar takardar kuɗin ya kai wata ɗaya. Ya ce kamata ya yi Babban Bankin Najeriya ya buga ƙarin sabbin takardun kuɗi kuma ya tabbatar sun shiga hannun jama’a.

Ya ce ya kamata a taƙaita yawan tsoffin kuɗin da ke hannun jama’a idan ana son wa’adin daina amfani da tsoffin nairorin ya tabbata.

Gabriel Daniel ya ce a ganinsa wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗi daga ranar 31 ga watan Disamba, ba abu ne mai yiwuwa ba.

Ya ce bai iya tunawa da karon ƙarshe da gani ko ya yi amfani da sabbin takardun ba, saboda hatta bankuna tsoffin kuɗi suke bayarwa a cikin banki da kuma na’urorin cirar kuɗi.

Mu ma ba mu da sabbin takardu – Mai POS

Wani mai sana’ar POS a Abuja, Halliru Ishaq ya ce ba shakka su ma sun lura da ƙarancin sabbin nairorin.

A cewarsa ko banki suka je karɓar kuɗi da wahala a ba su sababbi. “Na je banki bayan da dawowar tsoffin kuɗi ya fi sau nawa, amma duk kuɗin da na karɓo babu sabon kuɗi a ciki”.

Ya ce ko sabuwar takarda ɗaya, ba a haɗa musu a kuɗin da suke karɓowa a banki. “Don ni na karɓo naira 500,000 ya fi sau a irga, amma tun da nake zuwa ban taɓa karɓo sabon kuɗi ba”.

“Ko takarda ɗaya, ba za ka gani ba, duka tsofaffi za ka gani,” a cewar mai sana’ar POS ɗin.

Ya ce yanzu haka yana da kuɗi a wurin sana’arsa kimanin rabin miliyan, amma a ciki da wahala a samu sabbin nairorin da suka kai dubu goma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here