De Gea ya bar Manchester United bayan shafe shekaru 12 a kungiyar

0
137

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United David de Gea ya sanar da rabuwa da Club din nasa wanda ya shafewa shekaru 12 ya na taka masa leda a matsayin mai tsaron raga lamba daya a dukkanin gasa.

De Gea dan Spain wanda a kakar da ta gabata ya goge tarihin Peter Schmeichel a matsayin mai tsaron raga mafi doka wasanni masu yawa ba tare da an zura masa kwallo ba, ya lashe kyautar tauraron dan wasa da kuma kyautar dan wasa mafi soyuwa a wajen magoya baya tsawon shekaru 4 a jere.

Da tsakar ranar yau Asabar ne dan wasan mai shekaru 32 ya sanar da matsayar karshe kan rabuwa da Manchester United bayan gamuwa da gagarumin kalubale a kakar da ta gabata musamman ta yadda ya gaza karbar salon Manaja Erik ten Hag a fagen wasa.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa De Gea ya godewa magoya bayan Manchester United kan goyon bayan da suka nuna mishi da kaunar tsawon shekaru, inda ya ce yanzu lokaci ne da ya kamata ya bayar da wuri don tunkarar sabon kalubale a rayuwarsa.

Sakon na De Gea ya ci gaba da cewa “Manchester za ta ci gaba da samun gurbi a zuciyata, domin ita ta samar da ni kuma bata taba rabuwa da ni ba.”

A karshen watan Yuni ne kwantiragin De Gea ya kawo karshe da Manchester United inda bayanai suka ce dan wasan ya amince da tsawaitawa amma kuma kungiyar da kanta ta janye tayin da ta yi masa tare da sabunta wani marar armashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here