Alhazan Kano sun barke da gudawa a Makka

0
146

Kimanin alhazan jihar Kano tara ne suka ɓarke da guduwa a birnin Makka bayan kammala aikin Hajji.

Shugaban jami’an  kiwon lafiya na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) Dr. Usman Galadima ne ya tabbatar da hakan ranar Lahadi.

Dr. Galadima ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin jami’an yaɗa labaran NAHCON Ibrahim Abdullahi ya fitar.

Ya   ce alhazan sun haɗu da wannan larurar ne sanadiyyar cin abincin Takaru.

Likitan ya  ce binciken da aka gudanar a gidan da alhazan su ke ya tabbatar da cewa cikinsu ne ya ɓaci sanadiyyar wani  Dambu da suka ci.

Ya ƙara da cewa tuni jami’ansa suka shawo kan matsalar bayan da suka bai wa masu gudawar magunguna.

Ya kuma koka da yadda alhazan ke ci gaba da sayen abincin Tukaru duk da gargaɗin da ake yi musu.

Ba kwalara ba ce

Ya ce, “Alhazai sun nace cewa irin wannan abincin suka saba da shi a gida, yayin da wasu daga cikinsu ke cewa shi kaɗai za su iya saya bayan da suka ƙarar da kuɗin guzirinsu.”

Sai dai Dr Galadima ya ce wannan gudawar ba ta da alaƙa da cutar kwalara don haka ba a fargabar sauran alhazai zasu kamu da ita.

Ya kuma yi kira ga mahukunta da su fara bai wa alhazai abincin rana domin kare su daga sayen abincin Tukaru.

A yanzu dai hukumomi na bai wa alhazai karin kumallo da abincin dare ne kawai, in da ake ƙyale su su nemawa kansu na rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here