Za a soma karantar da dalibai da harshen gida a Nijar

0
153
Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi garambawul ga tsarin koyarwa a makarantun horas da malaman makarantar kasar.

Ta yi wannan garambawul din ne a wani yunkuri na inganta sha’anin ilimin makarantun boko na kasar.

A cikin sabon tsarin da ta fito da shi a halin yanzu, za a soma horas da malaman a cikin harsunan gida wanda hakan zai ba su damar amfani da harsunan wurin karantar da daliban a fannoni daban-daban.

Gwamnatin Nijar ta ce bisa binciken da kwararru suka yi a fannin ilimi, sun gano cewa tabarbarewar ilimin boko a Nijar na da alaka da yadda ake koyar da dalibai da harshen Faransanci zalla.

Hakan ne ya sa a halin yanzu gwamnatin Nijar din ta bayyana aniyarta ta soma amfani da harsunan gida wajen karantar da yara a makarantu inda za a soma horas da malamai domin su ma su nakalci yadda za su koyar da yara a makarantu.

Ana sa ran soma karantarwa da harsunan gida a makarantun firamare sai kuma sakandire inda a gaba ake son fadadawa har zuwa jami’a.

Tuni gwamnatin kasar ta soma gwajin wannan shirin a makarantun horas da malaman kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here