Tillaberi: Dubban mutane sun tsere daga muhallansu a Nijar

0
139

Kusan mutum 11,000 ne a yankunan da masu ikirarin jihadi suka yi kamari suka tsere daga gidajensu a wannan watan, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kasar.

“Wadannan mutane na tsere wa rikice-rikicen da kungiyoyin mayakan sa kai suke yi ne a yankin Tillaberi da kuma yankin da ya hada iyakokin kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali,” in ji Ofishin Kula da Jin Kai na MDD, OCHA a Niamey.

Hukumomin Nijar sun ce fiye da mutum 10,800 ne daga kauyuka tara a yankin Ouro Gueladjo “aka tilasta wa barin gidajensu daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Yuli.

Fiye da mutum 8,430 ne suke samun mafaka a garin Ouro Gueladjo da kuma wasu 2,140 a kauyen Torodi. Wasu mutum 215 kuma sun isa babban birnin kasar Niamey, mai nisan kilomita 70, in ji OCHA da hukumomi.

Hukumar ta MDD ta ce kashe wasu mutanen kauye biyu da aka yi ranar 3 ga watan Yuli ne ya jawo kaurar jama’ar, da kuma yadda kungiyoyin masu ta da kayar baya ke cin karensu babu babbaka inda suka ba su wa’adin kwana biyu su bar matsugunansu.

Majiyoyin kasar sun ce mutane da dama na kwana a makarantu cikin ajujuwa wasu kuma sun samu mafaka a wajen dangi da abokan arziki.

“Yanayin da mutane ke ciki ya tabarbare,” in ji OCHA, musamman ma a garin Ouro Gueladjo inda ake fama da karancin wajen zama da abinci da magunguna da ruwan sha.

Gwamnatin Nijar a ranar Laraba ta samar da tan 85 na abinci a yankin.

Ita ma hukumar OCHA na kokarin “samar da hanyar” da ma’aikatan agaji za su je Ouro Gueladjo inda aka kai dakarun sojoji don samar da tsaro.

Kungiyoyin ta da kayar bayan sun zafafa ayyukansu a kan mazauna karkara da suka hada da dasa nakiyoyi da kashe-kashe da satar mutane musamman a kan iyakar kasar da Burkina Faso, a cewar OCHA.

An shafe kusan shekara takwas babu zaman lafiya a yankin Tillaberi saboda ayyukan masu tayar da kayar baya da ke da alaka da kungiyoyin Al-Qaeda da IS.

Akwai kusan mutum 150,000 ‘yan gudun hijira a yankin, wanda girmansa ya kai na Koriya ta Kudu, in ji MDD.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here