Al-Hilal ta ware fam miliyan 300 don sayen Mbappe

0
198

Kungiyar Al-Hilal ta Saudi Arabiya ta samu izinin yin magana da Kylian Mbappe bayan tayi tayin kudi fan miliyan 259 kan dan wasan gaba na Paris St-Germain.

Kyaftin din Faransa mai shekaru 24, wanda saura shekara daya kwantiraginsa ya kare,ya ki sanya hannu kan tsawaita wa zakarun na Faransa.

PSG na son siyar da Mbappe a yanzu maimakon ganin ya tafi kyauta a bazara mai zuwa.

Komawar da Neymar ya yi kan fan miliyan 200 daga Barcelona zuwa PSG a shekarar 2017 shine ciniki mafi tsada a tarihi yanzu.

Idan ya koma Al Hilal Mbappe zai zama dan wasa na farko da aka saye mafi tsada a tarihin kwallon kafa inda zai zarce Neymar Jr.

Chelsea da Manchester United da Tottenham da Inter Milan da Barcelona duk sun nuna sha’awarsu kan Mbappe wanda a baya ya ce yana da niyyar barin PSG kyauta a karshen kakar wasa mai zuwa kuma ana ganin ya fi son komawa Real Madrid.

Hakan zai ba shi damar komawa Real Madrid ba tare da komai ba nan da watanni 12 idan ya yanke shawarar yin hakan.

Shugaban kungiyar Nasser Al-Khelaifi ya bayyana aniyarsa ta daukar matsaya mai tsauri akan Mbappe.

Al-Hilal dai na daya daga cikin kungiyoyin asusun zuba jari na jama’a na kasar Saudiyya.

Sun riga sun sayi Ruben Neves daga Wolves da Kalidou Koulibaly daga Chelsea a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here