Majalisa ta sanya batun bunkasa al`umma cikin manyan manufofinta

0
133

Majalisar wakilan Najeriya ta goma ta ce za ta sanya batun bunkasa al`umma ta ɓangaren tattalin arziki a cikin manyan manufofinta. 

Majalisar ta haɗa manufofin nata ne ta hanyar tattara ra`ayoyi daga `yan majalisar da kuma kwararru.

Majalisar ta ce ta lura da cewa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka…wanda shi ne ya sa ‘yan majalisar da kuma masana daga ɓangarori daban-daban suka haɗu suka kuma dukufa wajen yi wa tafiyar majalisar tsari da daidaita mata manufofi ta yadda za ta yi nasarar cimma su.

A taron, ‘yan majalisa da kwararru sun ba da gudummuwa wajen zayyana fannoni daban-daban dangane da ginshikan da ya kamata a gina manufofin majalisar a kan su, inda wasu daga ciki suka bayyana cewa yawan dogaron da Najeriya ta yi a kan man fetur wajen samun kuɗin shigarta, ya wargaza wa ƙasar lissafi, don haka ta na bukatar laluɓo hanyoyi don bunksa tattalin arziki domin gina rayuwar al`umma.

Sun jaddada cewa da wuya a samu kowane irin ci gaba, sai da zaman lafiya, kuma matsalar taɓarɓarewar tsaro na cikin manyan matsalolin da ƙasar ke fuskanta. 

Ginshikai shida ne dai majalisar wakilan ta goma ta yi anniyar gina manufofin nata a kan su, amma kuma suna da ‘ya’ya, sun haɗa da bunkasa tattalin arzikin al`umma da faɗaɗa shi, da samar da abubuwan more rayuwa da bunkasa ilimi da lafiya da yin tsari ta yadda gwamnati za ta din ga tafiyar da harkokinta ba wani nuku-nuku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here