Benzina: Macen farko da ta saka hijabi a gasar kofin duniya

0
112

Mai tsaron bayan Morocco, Nouhaila Benzina ta kafa tarihin zama ta farko da ta sa hijabi a gasar kofin duniya ta mata.

Mai shekara 25 ta saka hijabin a wasan farko da ta buga wa tawagar, wadda ta ci Koriya ta Kudu 1-0 a wasa na biyu a rukuni na takwas. 

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta amince a 2014 cewar mace ta rufe kanta kamar yadda addinin da take bi ya bukata,

Morocco ɗaya ce daga ƙasashe takwas da suka fara halartar gasar kofin duniya ta mata a karon farko da ake yi a Australia da New Zealand.

Benzina, wadda ke taka leda a Morocco, ita ce ta farko da ta saka hijabi a babbar gasar tamaula ta duniya a tarihi.

Ta yi zaman benci a wasan farko a rukuni na takwas da Jamus ta yi nasara da ci 6-0.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here