Gwamnatin Adamawa ta sanya dokar ta baci bayan debe kayan tallafi da matasa suka yi

0
73
Adamawa
Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya sa dokar ba-shiga ba-fita, ba-dare ba-rana a Yola babban birnin jihar sakamakon wasoson kayan tallafi da matasa suka yi.

Dokar da ya sanar ranar Lahadi ta fara aiki ne nan take.

Gwamnan ya ce hakan ya biyo bayan yadda matasan ke yawo da muggan makamai suna kai farmaki kan dukiyar al’umma a shaguna da gidaje.

Kafa dokar na nufin babu wanda za a amince ya yi zirga-zirga a titunan jihar Adamawa sai waÉ—anda ke ayyuka na musamman.

Gwamna Fintiri ya kuma roƙi al’umma da mazauna jihar su yi biyayya ga dokar domin duk wanda ya saɓa za a kama shi domin gurfanarwa gaban shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here