Yadda tsadar kudin makaranta ya jefa karatun dalibai cikin rashin tabbas

0
230

Duk da cewa mahukuntan Jami’ar Bayero Kano sun ce sun tsawaita wa’adin biyan kudin makaranta fiye da wata guda , a maimakon kwanaki 7 zuwa 10 da aka saba, har yanzu akwai dalibai da dama da ba su iya biyan kudin makaranta ba.

Wannan na zuwa ne sakamakon karin kudi da hukumomin jami’ar suka yi a kwanakin baya, lamarin da ya sanya dalibai tsaka mai wuya.

Hukumomin jami’ar sun ce sun yi karin ne saboda gwamnatin tarayya ta cire tallafin da ta ke bai wa jami’o’i.

Ranar 10 ga watan ogusta jamiar Bayero ta tsayar a matsayin ranar da za a rufe biyan kudin makaranta da sauran kudaden karatu a hukumance.

Sabon farashin kudin makarantar da tuntuni aka kara shi ya jefa karatun dalibai da dama a cikin rashin tabbass.

Wata daliba da ke karatu a jami’ar Bayero ta shaidawa BBC cewa ba ta san matsayin karatunta a jamiar ba.

”Ni daliba ce a jamiar Bayero Kano ina aji na biyu watau level 200, gaskiya har yanzu ban biya kudin makaranta ba, kuma bana tunanin zan yi . A ranar 10 aka ce za a rufe kuma ga shi har yanzu ban yi ba”, in ji ta.

Shi ma wani dalibi da ya kusan kamala karatu ya ce akwai abokansa da dama da suka hakura da karatun.

”Ina aji na uku, ina gab da fita, saboda haka ina ta fafituka wajan neman kudin makranta kuma ga shi har yanzu ban samu ba kuma ga shi su na gab da rufewa bakidaya”, in ji shi.

Bayanai sun ce akwai dalibai da dama masu kaifin basira wadanda ba su da karfin biyan kudin makaranta saboda tsada kuma da alama suna fuskantar barazanar hakura da karatun.

Wannan dalibin ya shaidawa BBC cewa ya na cikin daliban da ke fuskantar wannan barazana:

“Ina nema kasa ci gaba da karatu saboda wannan karin kudi, wanda kowane dalibi ana tsamanin da ya biya naira dubu dari biyu da talatin wanda a halin yanzu wannan kudin ba ni da su” .

Kawo yanzu ba bu wani karin bayani a kan ko za a kara wa’adin biyan kudin makarantar ko sassauci daga karin da aka yi.

Sai dai Malam Lamara Garba, jami’in hulda da jama’a na jami’ar Bayero ya ce suna tattaunawa da gwamnati kan yadda za a samar da wani tsari da zai taimakawa dalibai.

”Mahukutan jami’a suna tattaunawa da jami’an gwamnatin jihar Kano domin a samar da safa-safa wanda za su rika jigilar dalibai daga Naibawa zuwa Jami’a ,daga kuma can Kaba zuwa cikin jami’a da kuma bangaren hanyar Katsina zuwa jami’a”

“Game da batun ko jami’a za ta rika karbar kudi kadan-kadan har a gama, a gaskiya ba bu wannan tsarin.Kawai dai abinda jami’a ta yi shi ne a maimakon a rufe rajista cikin kwana bakwai zuwa 10 an buda shi yanzu kusan wata guda da wani abu. Kuma wannan ya isa kowa ya nemi kudi ya biya kudin makaranta”,in ji shi.

Karin kudin makarantar na zuwa ne a dai dai lokacin da jama’a ke ci gaba da kokawa game da karin kudin man fetur bayan janye tallafi, al’amarin da ya shafi bangarori daban -daban ciki harda batun sufuri wanda daliban ke amfani shi wajan zirga zirgar zuwa makaranta .

Sannan a gefe guda kuma bashin kudin karatu da hukumomin Najeriya suka amince da shi har yanzu bai fara aiki ba wanda ake ganin shi ne idan ya fara aiki zai yi wani tasiri ga rayuwar daliban da ke karatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here