Gwamnan Kano ya sake bude asibitin Hasiya Bayero da aka rufe

0
184

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake bude asibitin kula da kananan yara mafi tsufa a jihar, wanda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta rufe.

Bude Asibitin Hasiya Bayero a wannan karo na zuwa ne bayan shekaru 33 da bude shi karon farko, wanda kuma shi ne aiki na farko da Abba Gida-Gida ya kaddamar a cikin kwanaki 100 da karbar akalar jagoranci.

Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Yuni ne sabuwar gwamnatin Kano ta sanar da karbe asibitin da aka ce gwamnatin da ta gabata ta sayar wa wani mutum a kan kudin da ba su gaza Naira miliyan 6 ba, inda ta kaddamar da gyare-gyare domin a ci gaba da aiki da shi.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin a ranar Lahadi, Gwamna Abba Yusuf ya ce, asibitin na daya daga cikin asibitocin kula da kananan yara a fadin Arewacin Najeriya mai dauke da gadaje 86 da marasa lafiya kusan 5000 daga ciki da wajen jihar.

Ya ce wannan aiki da ya kaddamar wani nauyi ya sauke cikin jerin alkawuran da ya dauka tun yayin yakin neman zabensa.

Gwamnan ya kuma yi kira ga daukacin ma’aikatan lafiya da ke fadin jihar da su nuna kwazo da sadaukar da kai domin kuwa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani aiki na rashin da’a ko satar dukiyar jama’a ba.

A nasa bangaren, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero a lokacin da yake mika godiyarsa ga Gwamnan kan yadda ya kwato martabar ginin ya ce, “ba za mu manta da tarihin wannan wuri ba da muka taso muka gani ba tun muna yara.

“Muna rokon Allah Ya da kare shi, Ya kuma yi masa jagora wajen aiwatar da kyawawan ayyuka,” inji Sarki Aminu.

Wadanda suka halarci bude asibitin sun hada da Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo da Kwamishinan Lafiya, Dokta Abubakar Labaran Yusuf da wasu daga cikin ‘yan majalisar zartarwar jiha da wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Haruna Adamu da sauran masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here