‘Yan Boko Haram 78 sun mika wuya ga hukumar soji a Borno

0
128

Mayakan Boko Haram kimanin mutum 78 ne suka mika wuya ga rundunar soji a karamar hukumar Monguno da ke jihar Borno.

An baiyana cewa rundunar sojojin sun matsa musu da kai hare-hare, yayin da wannan harin ya jefa mayakan Boko Haram cikin matsanancin hali, farmakin da sojoji suka kai musu cikin makonni 2 ga sansaninsu guda 2, sojojin sun kashe musu mayaka 100 lamarin da ya sanya wasunsu mika wuya.

Rundunonin guda biyu na amfani da karfinsu da lafiyarsu wajen kaiwa junansu hari

Sau tarin lokuta kuwa yan ta’addan nakm kai harin mai kan uwa dawabi ta yadda basa ware kananan yara balle mata.

An samu bayanai daga majiyoyi na sirri da kuma wani kwararre gogagge a fannin yake, Zagazola Makama, ya bayyana cewa farmakin sosojin ya saka su zubar da makamai.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Agusta, 2023, kungiyar Boko Haram ta kama ‘yan ta’addar ISWAP kimanin 60 da suka hada da wasu manyan kwamandoji uku Abubakar Saddiq, Abou Maimuna da Malam Idris, a hanyarsu ta zuwa Damasak.

Daga baya sun kai manyan da suka aka kama zuwa wani gidan yari da ke Kwatan Mota kusa da Dogon Chuku, inda ake tsare da su a matsayin fursunonin yaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here