APC zata karbi mulkin Kano daga hannun NNPP – Barau Jibrin

0
291
Jibrin-Barau

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce jam’iyyar su ta APC za ta kwato mulkin jihar Kano daga hannun jam’iyyar NNPP mai mulki.

Jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Rabi’u Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ta lashe kujerar gwamna da kujerun sanatoci guda biyu a jihar a lokacin babban zabe, yayin da Barau, dan takarar jam’iyyar APC, ya lashe kujerar Sanata na uku.
A halin yanzu dai jam’iyyar APC a Kano tana kotun sauraron kararrakin zabe, inda take kalubalantar nasarar Abba Yusuf, gwamnan jihar mai ci.

Da yake magana a lokacin da tawagar mataimakan shugabannin kananan hukumomi (ALGOVC) a Kano suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba, Jibrin ya ce yana da kwarin gwiwar cewa kotun za ta yanke hukunci da APC zata dawo mulki.

“Muna addu’a kuma muna fatan sakamakon kotun ya yi mana kyau,” in ji Ismail Mudashir, mai magana da yawunsa.

“Komai yana hannun Allah. Mu hada kai mu yi aiki tare. In sha Allahu lokaci kawai muke jira, jihar Kano zata dawo hannun mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here