‘Yan sandan Birtaniya sun tuhumi tsohuwar minista Diezani da laifin rashawa

0
130
Diezani
Diezani

Hukumomin Birtaniya sun tuhumi tsohuwar Ministar Mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke game da zarge-zagren rashawa a kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya rawaito cewa, jami’an ‘yan sandan Birtaniya sun ce, sun tuhumi Alison-Madueke ne bayan sun zarge ta da karbar cin hanci, wanda aka ba ta a matsayin na goro bayan ta bayar da wata kwangilar harkallar man fetur da iskar gas ta miliyoyin kudi na fam.

Alison-Madueke mai shekaru 63, na cikin manyan jami’an gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Ta rike mukamin ministar mai daga shekarar 2010 zuwa 2015, yayin da ta zama shugabar Kungiyar Kasashen Duniya Masu Arzikin Man Fetur, OPEC.

Shugaban Hukumar Yaki da Miyagun Laifuka da Cin Hanci da Rashawa ta Birtaniya, Andy Kelly, ya bayyana cewa,

”Muna zargin Diezani Allison-Madueke ta yi amfani da karfin kujerarta a Najeriya, inda ta karbi cin hanci sakamakon kwangilar da ta bayar ta miliyoyin kudin fam.”

Tun lokacin da ta bar ofishinta, tsohuwar ministar ke ta fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ta sha musantawa.

Jami’an ‘yan sandan Birtaniya sun ce, a halin yanzu, Alison-Madueke na zaune ne a unguwar St. John’s Wood da ke yankin yammacin birnin London.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here