Kungiyar AU ta kori kasar Nijar daga cikin mambobinta

0
85

Kungiyar Tarayyar Afrika AU ta kori Jamhuriyar Nijar daga cikin mambobinta, abin da ke zama wani hukunci na baya-bayan nan da aka yanke wa kasar ta yammacin Afrika bayan juyin mulkin da sojoji suka yia watan jiya.


Bayan taron kungiyar a wannan Talata a birnin Addis Ababa na Habasha, kungiyar ta ce daukar matakin ya zama wajibi la’akari da yadda sojojin na Nijar suka ki bada hadin kan da ya dace a game da tattaunawar diflomasiya don magance rikicin siyasar kasar.

AU ta kuma gargadi dukkanin mambobinta da su guji aiwatar da duk wani mataki da zai halasta gwamnatin sojojin da suka kawar da shugaban farar hula Bazoum Muhammad.

Matakin na AU na zuwa ne bayan da tuni ECOWAS da wasu kungiyoyin kasashen ketare suka sanar da kakaba wa Nijar takunkumai wadanda tuni suka fara tasiri a kanta.

Sai dai kuma masana na ganin cire Nijar daga cikin AU ba zai yi mata wani tasiri ba, la’akari da yadda kungiyar ke zama tamkar dai ‘yar amshin shatan kasashen yamma a wasu lokutan.


Bayan wannan mataki, kungiyar ta AU ta kuma ce za ta bibiyi irin matakan da kungiyar ECOWAS ko CDEAO ta dauka kan Jamhuriyar Nijar don ganin ta inda ya kamata ta kara shiga da nufin kara matsa lamba ga sojojin na Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here