Jam’iyyar APC zata rabawa al’ummar jihar Kano kayan abinci – Abdullahi Abbas

0
212

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce jam’iyyar ta shirya baiwa ya’yanta da sauran al’ummar jihar kano tallafin kayan abinci a wannan watan azumin ramadana.

Abdullahi Abbas ya bayyana hakan lokacin da yake raba kayan abinci ga al’ummar yankinsa na Chiranci da Ɗiso, da Galadanchi da sauran unguwannin da yake makobtaka da su.

Ya ce tuni jagorancin jam’iyyar APC na jihar Kano suka haɗa ƙarfi da karfe don raba kayan abinci ga ahalin jam’iyyar a ranar Talata a ofishin jam’iyyar dake Kano.

Sannan yace kowacce karamar hukuma za ta amfana da tallafin wannan rabo da zata yi don jika maƙoshin yan jam’iyyar da kuma al’ummar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here