Amurka ta kara tattaunawa da Isra’ila kan kai agagi Gaza

0
189

Shugaban Amurka Joe Biden da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun tattauna ta wayar tarho game da halin da ake ciki a Isra’ila da Gaza, in ji fadar White House – karo na farko da suka yi hakan cikin sama da wata ɗaya.

“Shugaba Biden ya yi magana da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra’ila don tattauna sabbin abubuwan da ke faruwa a Isra’ila da Gaza, ciki har da halin da ake ciki a Rafah da kuma kokarin kara kai agaji ga Gaza,” in ji kakakin fadar White House.

Sun ƙara da cewa cikakken bayani kan tattaunawar tasu zai zo nan ba da jimawa ba.

Amurka ta kasance abokiyar kawancen Isra’ila kuma babbar mai ba da agajin soji, amma alaƙa na ƙara tsami tsakanin Biden da Netanyahu kan yaƙin Gaza, inda yanzu har ta kai bainar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here