Gobara ta kone motoci 8 da rumfuna a Kano

0
175

Hukumar kashe gobara reshen jahar Kano, ta tabbatar da tashin wata Gobara, a cikin wani Kangon gyaran Motoci, akan titin Lawan Dambazau, inda rumfunan Kanukawa 8 Suka kone.

Haka zalika wasu motoci guda 8 suma sun kone kurmus, sai kuma kayan aikin kanikawan da suma suka lalace.

Kakakin hukumar kashe gobara na jahar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari. ng, a ranar Talata.

Saminu Yusuf, ya ce sun karbi kiran waya daga ofishin Yan sandan Kwalli, da misalin karfe 2:15am na daren ranar Litinin, inda Yan sandan Suka shaida mu su tashin gobara a kan titin Lawan Dambazau kusa da Digar Jirgi a yankin karamar birnin Kano.

Ya Kara da cewa , jami’an su da suke kan aiki sun yi gaggawar zuwa wajen da lamarin yafaru , wadanda Suka tarar da cewar wani Kango ne , da ake amfani dashi a matsayin wajen Kanukanci da gyaran motoci, ne ya Kama da wuta.

Wuraren da suka Kama da wutar, sun hada da rumfuna 8 na kafintoci da motoci guda 8 na Kanukawa wadanda Suka kone kurmus.

Bayan haka an samu Rumfa daya da Mota 1, wadanda ba su kone sosai ba, sannan an samu nasarar takure wutar ba tare da, an barta ta yadu zuwa sauran wurare ciki harda wani masallaci.

Haka zalika akwai wasu motoci guda talatin 37 da suke ajiye da mota guda 1, wadanda ba su kone sosai ba.

Saminu Yusuf ya bayyana musabbabin tashin gobarar da tartsatsin wuta daga bangaren Kafuntoci, inda wutar ta yadu zuwa wajen Kanikawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here