Yan Najeriya sun nemi gwamnati ta sanya baki kan halin da suke ciki a Dubai

0
162

Tarin ‘yan Najeriya da ke rayuwa a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa ne yanzu haka suka tsinci kansu a tsaka mai wuya sakamakon yadda alaka tsakanin kasashen biyu ke kokarin tagayyara rayuwarsu.

Tun bayan matakin hadaddiyar daular Larabawa na daina baiwa ‘yan Najeriya visa da kuma kin sabunta takardun izinin aiki garesu, daruruwan ‘yan kasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika suka shiga gararamba cikin kasar ta yankin gabas ta tsakiya.

Jaridar Daily Trust ta zanta da wasu ‘yan kasar mazauna Dubai ta bayyana yadda kaso mai yawa daga cikinsu ke cikin hadarin yiwuwar rasa ayyukansu ba kadai a birnin na Dubai ba har ma da biranen Abu Dhabi da Sharjah.

‘Yan Najeriya sun zayyanawa Daily Trust irin tsangwamar da suke fuskantar a cikin kasar ta hadaddiyar daular larabawa, inda damarmaki da dama kan wuce sakamakon yadda gwamnatin kasar ta hana basu aiki, hatta ga wadanda suka shafe tsawon lokaci a cikin Dubai.

A zantawarsu da Daily Trust dimbin ‘yan Najeriyar sun bukaci gwamnati ta shiga tsakani don samar musu sassauci ga matsin da suke fuskanta a Dubai ta hanyar gyara alakar diflomasiyyar da ke tsakaninsu.

Sai dai masana na ci gaba da bayar da shawarwarin ganin ‘yan Najeriya sun kuma gida tare da amfani da fasaharsu wajen gina kasar maimakon ci gaba da fuskantar tsangwama da cin zarafi a Dubai.

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya bayar da tabbatar da daukar matakan gaggawa don warware rikicin da ya shafi huldar diflomasiyyar kasashen biyu.

Tun a shekarar 2021 ne alaka tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa ta samu nakasu bayan takaddama kan sauya lokutan jirage da kuma tafiye-tafiye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here