Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta shiga sahun masu kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da kamfanin mai na Shell daga gudanar da aikinsa a ƙasar har sai an samar da kariya ga mutanen Neja Delta.
Ƙungiyar ta ce ayyukan kamfanin na ƙara haifar da cin zarafin ɗan adam idan har ba a shawo kan matsalar gurɓata muhalli da kamfanin ke haifarwa ba.
Ƙungiyar ta ce dole ne kamfanin ya samar da wadatattun kuɗin da za a yi amfani da su wajen gyara gurɓacewar muhalli da ayyukansa ya janyo sannan dole a tuntuɓi mutanen yankin kan maganar sayar da kamfanin kan fiye da dala biliyan 2.4.
Masu fafutuka sun zargi Shell da hannu wajen yawan malalar mai a yankin Neja Delta da wasu matsalolin da suka janyo guracewar magudanan ruwa.
Gwamnatin Najeriya dai ba ta ce komai ba kan batun.
A baya kuma Shell, ya yi alƙawarin sabbin mamallaka kamfanin za su duba ɓarnar da aka yi.