Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken kudaden da gwamnatin Nasir el-Rufai, tsohon gwamnan jihar ta kashe.
Majalisar ta dora wa kwamitin alhakin bincikar kudaden tallafi da na lamuni da gwamnatin El-Rufai ta samu.
Haka kuma za ta bi diddigin kudaden da tsohuwar gwamnatin ta kashe wajen aiwatar da manyan ayyuka, a tsawon wa’adin mulkin El-Rufai, daga 2015 zuwa 2023.
Makonni biyu ke nan bayan a ranar 30 ga Maris, gwamna mai ci Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin Dala miliyan 587, Naira biliyan 85, da kuma kwangiloli 115 da ba a biya kudinsu ba daga El-Rufai.
Da yake magana a yayin wani taro, Gwamna Uba Sani ya kuma ce bai karni Aston ko kobo ba, tun da ya hau mulki a cikin watanni tara da suka gabata.
Ya ce, amma duk da haka, tulin bashin da El-Rufai ya bar masa na cin kaso mai yawa daga kudaden wata-wata da jihar ke samu daga Gwamnatin Tarayya.