Iran ta musanta ikirarin kai mata hari, ta ce ta lalata jirage 3 maras matuka na Isra’ila

0
210
Iran

Wani jami’in gwamnatin Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu wani harin makamai masu linzami da aka kai a cikin Æ™asarsu, yana mai Æ™aryata rahotannin kafafen watsa labaran Amurka da ke cewa Isra’ila ta kai musu hari.

An ambato kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran yana cewa ba a kai musu harin makamai masu linzami ba, inda ya Æ™ara da cewa na’urorinsu sun kakkaÉ“o jirage maras matuÆ™a da dama daga sararin samaniyar yankin Isfahan.

Sai dai jami’an gwamnatin Amurka biyu sun tabbatar wa CBS News cewa wani makami mai linzami na Isra’ila ya sauka a Iran. Reuters ya ruwaito cewa Isra’ila ta gaya wa Amurka shirinta na kai wa Iran hari.

Wasu jami’an gwamnatin Amurka da ba sa so a ambace su sun shaida wa CBS News cewa Isra’ila ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango a harin da ta kai wa Iran.

Wani jami’in Amurka ya shaida wa CNN cewa mahukunta a Washington ba su “amince” Isra’ila ta kai harin ba.

“Ba mu amince a mayar da martani ba,” a cewar jami’in gwamnatin Amurka. Jami’in ya tabbatar da cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka cewa za ta kai wa Iran hari nan da kwanaki masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here