Ma mallakin jam’iyyar NNPP ya zargi Kwankwaso da cin amanar sa

1
229

Wanda ya kafa jam’iyyar NNPP, Dr Boniface Aniebonam, ya ce matakin da Sanata Rabi’u Kwankwaso da ‘yan Kwankwasiyya suka dauka na kwace jam’iyyar, cin amana ne a gare shi.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Legas a ranar Juma’a, Aniebonam ya ce ya baiwa Kwankwaso dama a jam’iyyar ne domin cimma burinsa na siyasa na zama shugaban Najeriya .

Aniebonam ya ce shi kadai ya yi rajista tare da raya jam’iyyar NNPP daga shekarar 2002 zuwa 2022 har lokacin da Kwankwaso da tawagarsa suka same shi domin ya basu dama a jam’iyyar don yayi takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Ya ce: “Buba Galadima ne ya jagoranci tawagar da suka hada da Sen. Suleiman Hunkuyi da Farfesa Sam Angai zuwa gida na a Anambra, domin rokon mu mu karbi Kwankwaso a NNPP.

Bayan mun gama tattaunawa sai na yi wa Kwankwaso waya, bayan na yi masa tambayoyi kan manufarsa ga Nijeriya, sai na ba shi damar yin takara a jam’iyyar NNPP .

“Na yi imanin cewa Kwankwaso bai san me ake cewa rikicin cikin gida a jam’iyyar ba, har sai da ya fito fili a gidan talabijin, inda ya fito da sabon tambari da tutar jam’iyyar NNPP tare da chanza mana kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

“Abin damuwa ne kuma idan na ci gaba da yin shiru, hakan ba zai zama maslaha ga jam’iyyar ba, a matsayina na wanda ya kafa jam’iyyar a lokaci guda kuma shugaban kwamitin koli na jam’iyyar.

“Tsarin mulkin jam’iyyar ya ce duk wanda ya kafa jam’iyyar har karshen rayuwar sa yana cikin kwamitin koli na jam’iyyar, Amma dan uwana kuma abokina, Kwankwaso, yana son ruguza jam’iyyar da na gina tun daga 2002 zuwa 2022 shi da ya shigo da mu tsayar da shi takarar ya tsaya shugaban kasa a 2023.”

A cewarsa, “Na dauki nauyin jam’iyyar tsawon shekaru 22, kuma Kwankwaso yana son kwace ta daga gare ni daga cikin ta.

Yace zai Kalubalanci wannan matakin da Kwankwaso yake kokarin dauka na kwace masa jam’iyyar NNPP har zuwa gaban Kotu.

Wanda ya kafa NNPP ya ce da wannan mataki na daya, Kwankwaso ba zai sake jin dadin tsayawa takara a jam’iyyar NNPP ba, matukar ban yafe masa ba.

NAN

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here