Rundunar yan sandan jihar Kano, ta cafke mamallakin ginin benen nan mai hawa uku, da ya ruftawa mutane sama da goma a unguwar Kuntau, da ke ƙaramar hukumar Gwale, a ranar Juma’a.
Kakakin rundunar Æ´an Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce tuni rundunar Æ´an sandan ta fara gudanar da bincike akan faruwar lamarin, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da mamallakin ginin gaban kotu, domin fuskantar hukunci.
Ya Kara da cewa Rundunar zata yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar tsara Birane ta Jihar Kano domin ci gaba da gudanar da bincike akan yadda aka gaza bin ƙa’idojin da suka kamata wajen yin ginin benen.
A ranar Juma’a ne 26 ga watan Afrilun 2024, wani ginin bene mai hawa uku ya ruftawa Leburori sama da goma lokacin da suke aikin ginin benen, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku daga cikin su.