Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, bayan ƙudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.
Majalisar ta amince ta ƙudurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayyoyi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.
Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar.
A lokacin muhuwar, babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Peter Nwebonyi ya nemi majalisar ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyin, maimakon ɗaurin rai -da-rai.
A lokacin da aka nemi ra’ayin sauran ‘yan majalisar dangane da batun, majalisar ta nuna amincewarta kan dokar ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar.
To sai dai wasu tsirarun ‘yan majalisar ba su goyi bayan ƙudurin ba, inda Sanata Adams Oshimole ya kasance cikin masu nuna adawa da dokar.
To sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibril ya yi watsi da buƙatar sanata Oshimolen, yana mai cewa ƙorafin sanatan ya saɓa wa dokar majalisar saboda ƙorafin ya zo ne bayan majalisar ta amince da ƙudurin.