Bankin kasa CBN ya sanar da sabon farashin dala

0
105

Babban bankin kasa CBN ya sanar da sabon farashin da zai rika siyar da kowacce dalar Amurka daya ga masu Sana’ar canjin kudaden ketare.

Babban bankin yace daga yanzu zai rika siyarwa masu canjin kudaden ketare dala daya akan naira 1590, domin magance tazarar karancin dalar da ake samu a hada hadar dala ta na’ura.

Karanta karin wasu labaran:Majalisar wakilai ta umarci CBN ya dakatar da harajin tsaron intanet

Bankin ya fitar da sabon farashin a jiya wanda aka yiwa lakabi da canjin kudaden ketare don magance matsalar karancin kudaden ga daidaikun mutane masu bukatar yin ma’anala da dala.

CBN yace zai siyarwa kowanne kamfanin canjin kudaden ketare dala dubu 20 akan farashin na naira 1590.

Sai dai Bankin CBN yace mutanen da suka cancanta ne kadai zai siyarwa da dalar.

Amman CBN ya kafa dokar cewa duk wanda aka siyarwa da dalar ba zai dorawa mutane ribar data wuce kaso daya cikin dari ba idan zai siyar.

CBN ya umarci duk kamfanonin canjin kudaden ketare da suka cancanci a siyarwa da dalar da su tura kudaden su ga asusun babban bankin na kasa don samun damar siyan dalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here