Gwamnatin Taraba ta musanta cewa zata rushe babban masallacin Jalingo

0
49

Gwamnatin Jihar Taraba ta musanta labarin da wasu ke yadawa na cewa za ta rushe fadar masarautar Sarkin Takum da babban masallacin Juma’a, na Jalingo inda ta ce labarin bashi da tushe ballantana makama.

Gwamna Agbu Kefas, ne ya sanar da hakan ta bakin kwamishinar yada labarai ta jihar, Zainab Usman Jalingo.

Karanta karin wasu labaran:An bayar da belin tsohon gwamnan Taraba akan naira miliyan 150

Ta bayyana ikirarin a matsayin mara tushe, inda ta bayyana cewa an yi hakan don neman tada zaune tsaye.

Zainab, tace wadannan zarge-zarge gaskiya ba ne, tace sun mayar da hankali ne kan samar da shugabanci na gari da ci gaba mai dorewa ba batun addini ko kabilanci ba.

Ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar, wadda ta danganta su ga masu neman kawo hargitsi ga zaman lafiya a jihar.

Kwamishinar ta jaddada kudirin gwamnati na samar da zaman lafiya, hadin kai, ci gaba, da adalci ga daukacin mazauna jihar Taraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here