Kashim Shettima zai wakilci Tinubu a taron Commonwealth

0
56

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nigeria da za ta wakilci shugaba Bola Tinubu a wajen taron kasashe renon Ingila wato CHOGM 2024.

Shettima zai bi sahun Sarki Charles na Ingila da sauran shugabannin kasashen duniya daga mambobi 56 a taron wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Apia, da ke tsibirin Samoa wanda za’a fara daga 21 zuwa 26 na watan Oktoba.

Karanta karin wasu labaran:Darajar Naira za ta ci gaba da farfadowa – Shettima

Wata sanarwa da mai taimakawa Shettima kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha, ya fitar, ta ce shugabannin da za su halarci taron za su mayar da hankali kan manufar samar da makoma daya kuma mai kyau tsakanin mambobin kasashe rainon ingila.

Taken taron na bana zai mayar da hankali kan yadda mambobin kungiyar za su karfafa gwiwar juna wajen samar da ci gaba.

Sanarwar ta kara da cewa kasar nan da sauran kasashen duniya za su zabi sabon sakataren kungiyar kasashen na renon Ingila.

Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai yi amfani da damar wajen janyo hankalin masu zuba jari zuwa Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here