Surukar Shugaban Kasa, Zahra Bayero ta kammala karatu da digiri mafi daraja 

0
95

Matar Yusuf, Zahra Bayero Buhari ta kammala karatunta na digiri a bangaren kimiyyar gine-gine.

Kamar yadda surukarta kuma uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta wallafa a shafinta, Zahra ta gama ne da digiri mafi daraja.

Zahra, wacce ta kasance diya ga sarkin Bichi da ke jihar Kano, Alhajin Nasiru Ado Bayero ta kammala karatunta ne a fannin kimiyyar Gine-gine da digiri mafi daraja.

A cikin hotunan da ta wallafa, an gano Zahra tare da mijinta, Yusuf Muhammadu Buhari da kuma surukar tata, inda ta kasance sanye da kayan yaye dalibai.