Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya ce ba shi da wani zabi da ya wuce korar dubun dubatar bakin haure da ba su da izinin zama a kasar.
Cikin wata tattaunawa da Kafar yada labarai ta NBC a ranar Alhamis, yace basa tunanin abin da za su samu ko rasa bane.A cewar sa, za’a kori masu aikata laifuka a kasar da masu kashe mutane, ko cinikin kayan maye.
A shekarar 2021 aka dakatar da shirin kai samame kan wuraren ayyukan baƙin, wanda gwamnatin Trump ta aiwatar.
Adadin mutanen da ake kamawa a cikin Amurka tare da mayar da su ƙasashensu bai wuce 100,000 ba cikin shekara 10, amma sun kai har 230,000 a shekara a farkon mulkin Barrack Obama.