Sojoji sun kama masu daukar nauyin ‘yan ta’adda a Kaduna

0
96

Dakarun da ke aiki a runduna ta musamman ta ‘Operation Hadarin Daji’  sun kama wasu mutane 2 da ake zargin suna dukar nauyin ‘yan ta’adda a karamar hukumar Zaria ta jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

Rundunar ta bayyana haka, inda ta ce yaanzu haka ta kaddamar da farautar wani da ake kira AlhajAbubakar, wanda ake zargin yana taimaka wa ‘yan ta’ada da kudade.

Daraktan yada labaran shelkwatar tsaron Najeriya Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a game da nasarorin da runduna ta musamman din ta samu a fadin kasar, daga tsakanin 8 ga watan Satumba zuwa 22 ga watan.

Danmadami ya ce a bankin Access reshen PZ na Zaria ne aka kama wadanda ake zargin a yayin da suke kokarin ciro kudin ya kai Naira miliyan 14, wanda aka saka a cikin asusun ajiya na  Alhaji Abubakar.