Ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Bello Turji, yace cin amana ne harin da Sojojin Najeriya suka kai sansaninsa a jihar Zamfara.
Jaridar The Cable ta ruwaito yadda wani luguden wutan rundunar sojin saman Najeriya ya yi sanadin kashe gomman yan ta’adda a mafakar Turji.
Bayanai sun nuna cewa ‘yan fashin dajin sun halarci wurin ɗaura aure tare da Bello Turji lokacin da jirgin NAF ya yi ruwan bama-bamai a wani yankin ƙaramar hukumar Shinkafi.
Sai dai an ce Turji ya tsallake rijiya da baya. A wani faifan Audio da jaridar PRNigeria ta samu, ƙasurgumin ɗan bindigan ya nuna ɓacin ransa kan harin jirgin duk da ya amince ya watsar da ayyukan ta’addanci.
“Bamu kai hari ba an samu zaman lafiya tsawon watanni biyar amma yanzu da Sojoji suka farmaki gidanmu, muna jin an ci amanar mu musamman ganin yadda muka rasa mutane a harin Jirgin yaƙi.”
“Watanni 5 da suka shude bamu kai hari ko kashe mutun ɗaya ba a yankin Shinkafi. Sakamakon haka Noma da sauran harkokin kasuwanci sun fara farfaɗo wa ba tare da fargaba ba.”
“Na ji kunya da aka ambaci sunana bayan wasu ‘yan fashin daji da ‘yan ta’adda sun kai hari. Bayan gidana da aka tasa aiki, mafi yawan gidajen mutanen da ba ruwansu a Jejin harin jirgin ya taɓa su.”