Aƙalla mutum 24 ne suka rasu tare da lalata gida 16,625 a Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sakamakon ambaliyar ruwa da aka fuskanta a daminar bana ya zuwa yanzu.
Hukumar agajin gaggawa ta ƙasa reshen Katsina, SEMA, ta bayyana ranar Juma’a cewa ambaliyar ta kuma lalata gona 1,620 a yankunan Danja, da Ingawa da kuma Kafur.
Cikin wata sanarwa, kakakin hukumar Umar Muhammad ya ce an yi asarar kayan amfanin gona na miliyoyi sakamakon annobar.
Ya ce nan gaba kaɗan gwamnatin jihar za ta fara raba wa waɗanda abin ya shaf kayayyakin tallafi.
Jihohi da dama a Najeriya sun fuskanci ambaliya a wannan damina, wadda ta jawo rufe babbar hanyar da ta haɗa Abuja da Lokoja babban birnin Jihar Kogi mai maƙwabtaka.