Gurbatattun alluran da aka yi fasa kwaurinsu sun kashe yara 10 a Yemen

0
121

Akalla yara goma masu fama da cutar sankarar bargo sun mutu a wani asibiti na birnin  Sanaa, babban birnin kasar Yemen. Sun mutu ne bayan da aka yi musu allura mai dauke da  gurbatattun kwayoyi  da aka yi fasa-kwaurinsu, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a jiya ranar Juma’a.

Kasar Yemen dai na fama da daya daga cikin mafi munin rikicin jin kai a duniya, kasar Yemen na fama da karancin magunguna da kayan aikin jinya, sakamakon yakin da ya addabi wannan kasa mai matukar talauci a yankin Larabawa sama da shekaru bakwai.

Rikicin dai ya samo asali ne daga dakarun da ke biyayya ga gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan kawancen da ke karkashin makwabciyarta Saudiyya mai karfi, da ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran wadanda suka kwace iko da birnin Sanaa a shekara ta 2014.

A wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta ‘yan tawayen kasar ta fitar ta ce, “Yara goma da ke dauke da cutar sankarar bargo sun mutu” a asibitin Kuwait, inda ta ce suna cikin rukunin marasa lafiya 19 masu shekaru tsakanin uku zuwa 15 da ke fama da cutar, wadanda kuma yanayinsu ya tabarbare saboda “rashin lafiyar cutar sankarau.