Rikicin Boko Haram ya lakume rayuka dubu 100 da sama da naira tiriliyan 3 – Irabor

0
82

Hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya bayyana cewar rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 100 tare da asarar dukiyar da ta zarce naira tiriliyan 3 da miliyan dubu 240 tare da raba mutane sama da miliyan 2 daga muhallinsu.

Irabor ya gabatar da wadannan alkaluma ne lokacin da yake jawabi ga taron bitar da majalisar ministocin Najeriya ta kammala, wanda ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan takaran shugaban kasar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.

Babban hafsan ya kuma ce dakarun Najeriya sun yi nasarar murkushe rikicin boko haram zuwa takaitaccen wuri a yankin arewa maso gabashin Najeriya, duk da yake wasu daga cikin mayakan sun sauya wuri zuwa yankin arewa maso yammacin kasa.

Janar Irabor yace rundunonin sojojin kasar sun karbi kudin da ya kai naira triliyan 2 da rabi a cikin shekaru 7 daga kasafin kudin Najeriya wanda ya taimaka sosai wajen gudanar da ayyukan tsaron cikin gida.

Sai dai yace abin takaici shine wannan adadi shine kashi 35 na kudin da sojojin ke bukata domin gudanar da ayyukan su da kuma sayan makaman zamani.