Gwamnati ta daukaka kara kan sallamar Kanu da kotu ta yi

0
75

Gwamnati ta daukaka karar ne tana zargin Kanu da ta’addanci da cin amanar kasa.

A makon jiya ne alkalan kotun guda uku, karkashin jagorancin Mai Shari’a Jummai Hanatu Sankey suka yi watsi da sauran laifuffuka bakwai da gwmanati ta zargi Kanu da aikatawa, bisa hujjar take dokar kasa da kasa yayin kamo shi daga Kenya.

Sai dai Babban Lauyan Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce sallamar Kanu kawai kotun ta yi amma ba ta wanke shi daga laifuffukan da ake zargin sa da su ba kafin tserewarsa a Satumba, 2017.

A cikin karar da ta shigar Kotun Koli ranar Talata, gwamnati ta ce Kotun Daukaka Kara ta yi kuskure wajen soke sauran laifuffukan da ake zargin Kanu da su, inda ta ce Babbar Kotun Tarayyar da aka shigar da karar da farko ba ta da hurumin sauraren karar.